Dan Najeriya ya kirkiro na'urar auna numfashi

Na'urar auna numfashi
Image caption Na'urar auna numfashi

Wani dalibi dan Najeriya wanda ke yin karatun digirinsa na uku a Birtaniya ya kago wata na'ura wadda za ta iya saukaka wa likitoci auna numfashin marar lafiya.

Wanda ya kago wannan na'ura, Abdulkadir Hamidu Alkali daga arewacin Najeriyar, injiniya ne da ke karatun digirin digirgir a Jami'ar Sheffiield Hallam.

Ya kago na'urar ce bayan da wani asibiti na kananan yara ya bayyana kasa samun biyan bukata daga na'urorinn da ake da su a yanzu, musamman wajen auna lumfashin kananan yara.

Bayan da injiniyoyi suka yi kokari a baya ba tare da nasara ba, Malam Abdulkadir Hamidu Alkali ya sami nasarar kago na'urar da za ta iya biyan bukata ba ma tare da taba jikin yaron ba.

Karin bayani