Nijeriya da Somalia sun dawo da hulda

Image caption Hassan Sheik Mahmud, shugaban Somalia

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar Somalia na cewa, an dawo da huldar diplomasiyya tsakanin Somalia da Najeriya.

Tuni dai jakadan Najeriya a Somaliar, Akin Oyeteru ya mika takardun soma aiki ga shugaban kasar Somalia.

Kasashen biyu sun ce zasu tallafawa juna ta fuskar yaki da ta'addanci da kuma ayukan samar da zaman lafiya a Somalia.

Sanarwar ta kuma ce, Nijeriya zata taimakawa Somalia wajen yaki da kungiyar Al Shabaab wacce suka ce tana da alaka da kungiyar Boko Haram.