Thailand: Tashin hankali ya ƙazanta

Image caption Masu zanga-zanga a Thailand

A Thailand tashin hankali na cigaba da zafafa yayin da ake arangama tsakanin magoya bayan gwamnati da kuma magoya bayan masu adawa da gwamnatin.

An dai kai hari ne akan wasu dake kan hanyarsu ta zuwa domin shiga zanga-zangar nuna goyon bayan gwamnati, kuma lamarin ya kai ga mutuwar mutum guda.

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu irin wannan arangama tun da aka soma tarzomar nuna kin jinin gwamnati a kasar.

Tuni dai masu zanga-zangar adawa da gwamnatin suka mamaye ma'aikatun gwamnati da dama a yunkurinsu na kifar da gwamnatin, Pra minista, Yinluck Shinawatra.