'Yan adawar Syria sun rasa samun taimako

Taron baiwa yan adawar Syria taimako
Image caption Taron baiwa yan adawar Syria taimako

Amurka da Birtaniya sun jingine taimakon da suke ba kungiyar 'yan adawa ta Syria da kasashen yamma ke goyan baya, wato Free Syrian Army da ke arewacin Syria.

Tallafin ya hada da magunguna da kayayyakin sadarwa da abinci da janareta.

Kasashen sun dau wannan matakin ne bayan da 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama suka kwace sito-sito din makamai mallakar kungiyar 'yan adawar ta Free Syrian Army ran juma'ar da ta wuce.

Wakilin BBC ya ce kungiyar wadda ake kira kasar Islama ta Iran da Syria ko kuma ISES ta kunshi yawancin masu jihadi ne da sukai tururuwa zuwa Syria daga kasashen waje daba-daban.

Amurka ta yi alkawarin basu wadannan kayayyaki da kudinsu ya kai kusan dala miliyan dari biyu da hamsin.

Amurka ta ce jinginar da tallafin ba zai shafi agajin jin kai da suke bayarwa ba ba, wanda kungiyoyin bada agaji ke shiryawa.