Jam'iyyar APGA ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Anambra

anambra
Image caption Masu zabe a jihar Anambra

Hukumar zabe a Najeriya ta bayyana dan takarar jam'iyyar APGA cif Willie Obiano a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra wanda aka karasa a jiya asabar .

Dan takarar jam'iyyar PDP Tony Nwoye shi ne ya zo na biyu, yayinda dan jam'iyyar APC Senata Chris Nngige ya zo na uku, shi kuwa dan takarar jam'iyyar Labour Ifeanyi Uba ya zo na hudu.

Sakamakon zaben be zo wa galibin jama'a da mamaki ba, saboda yadda 'yayan jam'iyyar APGA suka yi ammanar cewa dan takararsu ne dake kan gaba zai cinye zaben.

Shi kuma dan takarar jam'iyyar PDP Tony Nwoye wanda shi ne na biyu kan iya samun nasara ko a kada shi.

Sai dai 'yan jam'iyyar APC da Labour ba su shiga karashin zaben ba, saboda suna zargin cewa ba'a shirya zaben yadda ya kamata ba kuma suna bukatar a gudanar da sabon zabe.

Ha ka kuma wasu suna shirin daukar mataki zuwa kotu domin su shigar da koke.