Dakarun Faransa sun isa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

cental africa republic
Image caption Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Ma'aikatar tsaro a birnin Paris ta ce dakarun Faransa sama da dari biyu sun isa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Su ne dai kashin farko da Faransa ta tura a kokarin farfado da zaman lafiya a kasar.

Nan ba da jimawa ba za a tura karin wasu dakarun daga Jamhuriyar Congo.

Wakiliya ta musamman a kungiyar Tarayyar Afrika ta shaida wa BBC cewa dakarun Afrika suna ta aiki na taimakawa a daidaita al'amura a kasar.

Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na fuskantar tashe tashen hankula tun bayan da 'yan kungiyar 'yan tawaye ta SELEKA suka karbe iko a Bangui babban birnin kasar.