Jikan Mandela zai fuskanci tuhuma

Image caption Mandla Mandela, jikan Nelson Mandela

Hukumar shari'a ta Afirka ta Kudu ta ce za ta tuhumi daya daga cikin jikokin Nelson Madela da laifin cin zarafi tare da yiwa wani mutum barazana da makami.

Jikan na Mandela Mandla Mandela zai gurfana a kotumand ranar Juma'a mai zuwa.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ce tuhumar ta danganci cin zarafi ne da Mandla ya yiwa wani malamin makaranta.

Sai dai wani mai magana da yawun Mandla Manelan ya ce ko kadan lamarin bai faru ba.