Mutane hudu sun hallaka a hadarin jirgin kasa a New York

hadarin jirgin kasa a New York
Image caption hadarin jirgin kasa a New York

Wani jirgin kasan pasinja mai zirga zirga a cikin gari a gundumar Bronx dake birnin New York na Amirka ya goce daga layin dogo.

Akalla mutane hudu sun rasu wasu kimanin sittin kuma sun sami raunuka.

Gwamnan New York Andrew Cuomo da yake jawabi a wurin da hadarin ya faru yace mutane goma sha daya suna cikin matsanancin hali kuma matukin jirgin na daga cikin wadanda suka ji rauni.

Taragai hudu ne na jirgin suka jirkice. Mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce sun firgita kwarai da aukuwar hadarin.

Karin bayani