Majalisar Dokokin Somlia na muhawara

Image caption Majalisar dokokin Somlia na muhawara kan Abdi Farah

'Yan majalisar dokokin Somalia sun fara muhawara akan wani daftari na kada kuri'ar rashin amanna akan Firaministan kasar Abdi Farah Shirdon wanda ya bata da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmoud.

A baya bayan nan ne Mr Shirdon ya soki shugaban kasar wanda ya baiyana cewa baya aiki da ka'idojin kundin tsarin mulki.

Magoya bayan shugaban kasar sun zargi Firaministan da rashin iya gudanar da aiki.

Masu aiko da rahotanni sun ce rarrabuwa dake faruwa a tsakanin gwamnatin Somaliar ka iya raunata yunkurin daidaita kasar wadda ke fama da rikici fiye da shekaru ashirin da suka wuce.

Karin bayani