Shinawatra ta ce babu zancen yin murabus

Image caption Masu zanga zanga na bukatar Shinawatra ta yi murabus

Firai Ministar Thailand Yingluck Shinawatra ta yi watsi da bukatun 'yan adawa na sai ta yi murabus, yayinda mummunan tashin hankali ke ci gaba da gudana a wajen gine ginen gwamnati

Yingluck Shinawatra tace kofar ta a bude take domin tattaunawa, bayan wata ganawa tare da jagoran masu zanga zanga

Sai dai ta ce bukatar maye gurbin gwamnatin ta, da wani kwamiti da za a nada ya saba kundin tsarin mulki.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta yin amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashen roba domin korar mutanen dake kokarin keta shingen da aka sanya masu a wajen gidan Gwamnati