Ana ci gaba da zanga-zanga a Ukraine

Ukraine protest
Image caption Masu zanga-zanga a Ukarine

Idan an jima a yau ne ake sa ran gwamnatin Ukraine da shugabannin 'yan adawa za su soma tattaunawa bayan kwanakin da aka shafe ana zanga-zanga a Kiev babban birnin kasar.

Kakakin Majalisar

dokoki ta kasar Vlodymry Rybak ya yi alkawarin cewa za'a ba dukannin bangarorin damar bayyana ra'ayoyinsu.

Masu zanga -zanga sun hau kan tituna ne bayan da shugaba Viktor Yanakovych ya ki sa hannu a kan yajejeniyar kawance da Tarayyar Turai.

Sai dai har yanzu daruruwan masu fafutuka na ci gaba da zama a sansanonin da suka kafa a birnin Kiev.

Mutane dubu dari daya zuwa dubu dari biyar ne dai ke zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnatin.

Sai dai an yi taho-mu-gama a wani wuri kusa da fadar shugaban kasa tsakanin masu zanga-zangar da jami'an 'yan sanda

Haka kuma da dama daga cikin masu zanga zangar sun ji raunuka kuma hukumar 'yan sanda ita ma ta ce jami'anta kusan dari daya sun ji raunuka