Ukraine: Zanga-zanga ta ƙazanta

Masu zanga zanga a Ukraine sun mamaye babban zauren taro dake Kiev babban birnin kasar.

Kuma masu zanga-zangar sun yi kokarin afkawa fadar shugaban kasar a gangamin adawa mafi girma domin nuna kin jinin shugaban kasar Viktor Yanukovic.

Su dai mazu kin jinin gwamnatin suna yi ne saboda gwamnatin ta ki amincewa ta sanya hannu akan wata yarjejeniyar kawance da kungiyar tarayyar turai.

Tun da farko mataimakin shugaban majalisar turai Jacek Protasiewicz ya bi sahun yan zanga zangar inda ya yi jawabi ga taron gangamin.