'Amfani da jirgi marar matuki wajen aika kaya'

samfurin yadda jirgin yake
Image caption Yanzu kamfanin yana cikin jarraba yadda zai rika amfani da wannan fasaha

Kamfanin sayar da kaya ta intanet mafi girma a duniya yana jarraba yadda zai rika amfani da kananan jirage marassa matuka wajen aika kayayyakin da aka saya a kamfanin har gida.

Kananan jiragen masu suna Octocopters za su iya kai kayan da nauyinsu ya kai kilogram 2.3 ga wadanda suka saya cikin minti 30 da saye.

Sai dai shugaban kamfanin Jeff Bezos wanda ya bayyana haka ya ce za a iya kaiwa nan da shekaru biyar kafin a fara amfani da wannan fasaha.

Mr Bezos ya ce za a kira tsarin Prime Air kuma kamfanin yana shirin bullo da shi ne yayin da yake kokarin bunkasa harkokinsa.

Haka kuma hukumar kula da zirga zirgar jirage ta Amurka har yanzu ba ta bayar da izinin amfani da jirage marassa matuka don amfanin farar hula ba.