Kungiyar Malaman Jami'o'i ta maida martani

nigeria,universities,strike
Image caption Malaman jami'o'i dake yajin aiki a Najeriya

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ce kan 'ya'yanta a hade yake dangane da yajin aikin da ta kwashe watanni biyar tana yi.

Kungiyar dai tana maida martani ne ga wasu rahotanni dake cewa wasu daga cikin mambobin kungiyar sun yanke shawarar komawa bakin aiki.

Hakan ya biyo bayan barazanar korar da gwamnatin kasar ta yi musu.

Shugaban kungiyar Malam Nasiru Isa Fagge ya shaidawa BBC cewa adadin mambobinsu masu ra'ayin komawa bakin aiki bai taka-kara ya karya ba.

Ya kuma ce suna nan a kan bakansu na ci gaba da yajin aiki har sai an biya musu bukutansu.