An kawo karshen rikicin fili da ya shafi Dangote

Dangote Najeriya
Image caption Aliko Dangote

Rikicikin da ake yi a kan fili tsakanin iyalin wani babban malami a kasar Senegal da hamshakin me arzikin nan na Najeriya Aliko Dangote ya zo karshe.

Kamfanin Dangote ya biya biliyan 6 na CFA a matsayin diyya ga iyalin marigayi Serigne Saliou, abin da kuma ya kawo karshen gwagwarmayar da aka shafe fiye da shekara guda ana yi a gaban kotu.

Manyan masu fada aji a kasar ne suka nemi shugaba Macky Sall ya shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu.

Ko da yake daya daga cikin 'ya'yan marigayi Serigne Saliou ya yi zargin cewa shugaba Sall na goyon bayan Aliko Dangote.

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin kasar ya musanta zargin.

Yanzu diyyar da aka biya za ta ba kamfanin damar samar da siminti.

Dangote ya yi alkawarin samar da guraben ayyukan yi dubu uku a kasar ta Senegal.