Ghana ta zargi Ivory Coast da yunkurin kisa

John Mahama
Image caption Rahotan ya ce wani mutum da ke goyan bayan Mr Gbagbo da ya koma Ivory Coast din ya bace bat.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mahukuntan Ghana sun fada mata cewa Ivory Coast ta tura wakilanta Ghana don su kashe magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Ggagbo ko kuma su kama su.

Wani rahotan Majalisar, ya ce gwamnatin Ghana ta fada wa masu sa ido cewa sau biyu a wannan shekarar tana ganin hakan.

Rahotan ya ce wani mutum da ke goyan bayan Mr Gbagbo da ya koma Ivory Coast din ya bace bat, ba'a ji duriyarsa ba.

Har ila yau rahoton ya ce gwamnatin Ivory Coast ta biya dakarun sa kai da ke goya bayan Gbagbon a Liberiya da ke makwabtaka da kasar na kada su kai hari a kan iya kar.

kotun manyan laifuka ta duniya na tsare da Mr Gbagbo, akan tuhumarsa da aikata laifuka akan biladama.