Yunkurin hallaka magoya bayan Gbagbo

Laurent Gbagbo
Image caption Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na tsare da Mr Gbagbo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mahukuntan kasar Ghana sun fada mata cewa gwamnatin Ivory Coast ta tura wakilanta Ghana don imma su kashe magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Ggagbo ko kuma su kama su.

Rahotan ya ce wani mutum dake goyan bayan Mr Gbagbo da ya koma Ivory Coast din ya bace bat, ba'a ji duriyarsa ba.

Har ila yau rahotan ya ce gwamnatin Ivory Coast ta biya dakarun sa-kai dake goya bayan Gbagbon a Liberiya dake makwabtaka da kasar na kada su kai hari a kan iya kar.

Yanzu haka dai kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na tsare da Mr Gbagbo, inda ake tuhumarsa da aikata muggan laifuka akan bil adama.

Karin bayani