Dan Nigeria Isa Mu'azu ya koma Burtaniya

Isa Mu'azu
Image caption Jirgin dake daukar Isa Mu'azu ya shafe sa'oi a sararin samaniya

Dan Najeriyar nan Isa Mu'azu ya koma Burtaniya bayan da aka tilastawa jirgin da yake ciki juyawa daga Najeriya.

Lawyoyin Isa Mu'azu wanda yaki cin abinci har tsawon kwanaki 100, sun ce ya dawo zuwa cibiyar da ake tsare da shi ta Harmondsworth a Birtaniya.

Ana tunanin cewa hukumomin Najeriya basu baiwa jirgin dake daukarsa iznin sauka bane, amma hukumomin Nigeriar sun musunta.

Mr. Mu'azu ya nemi mafaka a Burtaniya, yana mai cewa masu tsautsauran ra'ayin addinin Islama a Najeriya zasu kashe shi.

Jam'iyyar Labour dai ta ce gwamnatin Najeriyar nada tambayoyin da ya kamata ta amsa.

Sai dai ma'aikatar cikin gida a Burtaniyan ta yi watsi da dalilansa, sannan ta yi yunkurin tusa keyar Mu'azu mai shekaru 45 a duniya a ranar Juma'a.

Jirgin da aka yi shata wanda ke daukar Mu'azu ya shafe sa'oi da dama a sararin samaniya, amma an yi imanin cewa hukumomin Najeriyar basu bashi iznin 'yancin sauka bane. Ba'a dai san ko menene dalili ba.

Ana tunanin jirgin ya tsaya a Malta na sa'oi biyu kafin ya komo Burtaniya.

'Yajin cin abinci'

Lawyoyinsa sun ce Mu'azu ya koma bangaren kula da marasa lafiya a Harmondsworth.

Ma'aikatar cikin gidan Burtaniya ta ki cewa komai akan abinda ya faru, amma an fahimci cewa jami'anta na aiki tare da gwamnatin Najeriya domin kokarin ganin an fitar da shi.

Isa Mua'azu dai ya kasance a tsare ne tun lokacin da yai ikirarin neman mafaka a watan Yuli, yana mai cewa yana fuskantar barazana daga Kungiyar Boko Haram

Ya kuma shiga cikin Burtaniyan a matsayin bako a watan Yulin shekarar 2007, kuma ya zauna ba tare da izini ba bayan da takaddar iznin zaman sa wato visa ta kare a watan janairun shekara ta 2008

Karin bayani