Hadarin jirgin kasa na New york

Newyork train
Image caption Jirgin kasan da ya yi hadari a Newyork

Masu bincike a Amurka sun ce jirgin kasa nan da ya yi hadari a New York, inda mutane hudu suka mutu , na gudu ne sosai lokacin da lamarin ya faru.

Sun ce jirgin kasan na tafiya ne a kan kilomita 130 a kowace awa, abin da ya ninka gudun da ya kamata ya rika yi bisa ka'ida

Jirgin ya yi hadari ne lahadin da ta gabata lokacin da yazo yin kwana kusa da kogin Hudson, inda ya kamata ace ya rage gudu da kilomita 50 a kowace sa'a.

Hukumar kiyaye hadura ta ce ba ta da masaniya a kan ko jirgin na da matsalar birki.

Mutane fiye da 60 ne suka ji raunuka a cikin hadarin, ciki har da direban jirgin.

Masu bincike sun soma yi masa tambayoyi tare kuma da bincikar wayarsa ta salula