Zanga-zangar Bangkok ta dau sabon salo

Thailand
Image caption Masu Zanga-zanga a Bangkok

Hukumomi a kasar Thailand sun janye kariyar da suka sanya a gaban ginin hedikwatar 'yan sandan kasar da ke Bangkok.

Sun kuma fadawa masu zanga-zangar cewar suna iya shiga idan suna so.

Ginin dai shi ne na baya-bayan nan da masu zanga-zangar ke son su mamaye.

Wakilin BBC ya ce yunkurin da hukumomi suka yi na da nufin kunyatar da Shugabannin masu zanga-zangar wadanda ke kokarin tsokanar karin wata arangama.

Fira ministar kasar Yinluck Shinawatra ta yi watsi da bukatar masu zanga-zangar cewa a maye gurbin gwamnatinta da wata majalisa wadda ba zababbiya ba ce.