Ukraine:Zanga-zangar da ake yi alamace ta juyin mulki

Ukraine
Image caption Masu zanga-zanga a Ukraine

Fira ministan Ukraine Mykola Azarov ya ce zanga-zangar da ake ci gaba da yi a kasar ta nuna alamomi ne na juyin mulki.

Dubban masu fafutuka 'yan adawa suna babbake gine-ginen gwamnati tare da mamaye babban dandalin taro na Kiev babban birnin kasar.

Masu zanga-zangar sun nemi Mr Azarov da Shugaba Viktor Yanukovich su sauka daga mulki saboda ki da suka yi ta amincewa da yarjejeniyar kawance da Tarayyar Turai.

Shugabannin jam'iyyun adawa sun yi kira da a kada kuri'ar yanke kauna da gwamnatin a yau Talata.

Shugaban kasar ya gaya wa masu zanga-zangar su kiyaye doka, yana cewar zai tashi zuwa kasar China don wata ziyara da dama can aka shirya zai kai a kasar.