Joe Biden zai gana da Xi Jinping

Image caption Amurka da China za su tattauna kan sararin samaniyar Asia

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden zai isa Beijing a ziyarar da yake yi ta baya-bayan nan a yankin Asia, wadda ta bada karfi kan rashin jituwa tsakanin China da Amurka da sauran kawayenta na yankin.

Mr Biden ya ce zai tattauna da shugaban China Xi Jinping don nuna damuwa akan ayyana sabon sararin samaniya da Sin din ta yi wanda ke tsuburin da ake takaddama akai da ke gabashin tekun China da ita ma Japan ta ce yankinta ne.

Da yake jawabi a jiya Talata a Tokyo,Mr Biden, ya soki abinda ya kira wani yunkuri na kashin kai da China ta dauka domin sauya yadda yankin yake tun da farko.

Mr Biden ya kuma kara da cewa Amurka za ta tsaya tsayin daka akan muradin kawayenta da kuma Japan.

Karin bayani