Alkalai sun yi watsi da yiwuwar baiwa Arafat guba

Yaseer Arafat
Image caption Hukumar mulkin Falasdinawa ta ce nan gaba kadan kwararrunta za su yanke hukuncinsu

Wasu Alkalai da kotunan Faransa suka nada domin gudanar da bincike a kan mutuwar tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat a shekara ta 2004, sun yi watsi da hasashen da ake yi cewa an kashe shi ta hanyar ba shi guba.

Alkalan sun ce mutuwar Allah da Annabi ce Mr Arafat din ya yi.

Sun ziyarci Gabar Yammacin kogin Jordan inda aka kai Yasser Arafat din a lokacin da ya fara rashin lafiya, kafin daga bisani a tafi da shi Faransa domin yi masa magani.

Hukuncin Alkalan dai ya saba wa sakamakon binciken da wasu kwararru suka gudanar a Switzerland a watan jiya, wanda ya ce mai yiwuwa gubar Polonium ce ta kashe Mr Arafat.

Hukumar mulkin Falasdinawa ta ce nan gaba kadan kwararrunta za su yanke hukuncinsu a kan wannan batu inda za su bayyana mutanen da suke ikirarin sune keda hannu a mutuwar Mr Arafat.

Karin bayani