Jirage marasa matuka a Congo

Image caption Jirgi marar matuki

Ofishin ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya soma tura jiragen sama marasa matuka domin yin sintiri a kan iyakar kasar da Rwanda da kuma Uganda.

Wannan ne karon farko da Majalisar ke yin amfani da irin wadannan jirage.

Zasu rika sa ido kan abubuwan dake gudana a kan iyakar kasar daga bangaren gabas wadda ke da yawan dazuka.

An dade ana zargin cewa 'yan tawaye na amfani da wadannan hanyoyin wajen samun makamai, ciki har da kungiyar M23 wadda aka murkushe a baya bayan nan.

Rahotanni masu yawa na Majalisar Dinkin Duniya sun zargi kasashen Rwanda da Uganda da taimakawa 'yan tawayen M23.

Dukan kasashen biyu sun musanta zargin.

Da farko za a tura jirage biyu ne marasa matuka, kirar Italiya, zuwa yankin.