An maido da layukan salula a Maiduguri

Image caption Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno dake arewacin Najeriya sun nuna cewa an maido da layukan wayar salula a birnin Maiduguri da kewaye.

Jihar dai na daya daga cikin jihohi ukun da aka sanya wa dokar ta baci a watan Mayu saboda tabarbarewar tsaro.

Tuni dai aka maido da wayoyin sadarwa a jihohin Adamawa da Yobe da ke makwabtaka da Bornon

A halin yanzu mutane na iya kiran 'yan uwansu da ke jihar bayan shafe watanni ba tare da sada zumunci ba.

Matakin dawo da wayoyin sadarwar na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan Boko Haram suka kaddamar da munanan hare-hare a cibiyoyin jami'an tsaro da ke Maiduguri.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya kafa dokar ta baci a jihohin Adamawa da Yobe da kuma Borno don murkushe ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram.

Karin bayani