Hunturu na yi wa yaran Syria barazana

Image caption Yaran Syria fiye da miliyan hudu na bukatar abinci da makwanci

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi gargadin cewa Kananan yaran Syria na tsananin fuskantar kamuwa da sanyi yayinda hunturu ke karatawo.

Haka kuma yawan Yaran da akai kiyasin cewa suna cikin matukar bukata sun karu tun daga shekarar data gabata.

Yara fiye da miliyan hudu na bukatar abinci da makwanci, kuma yara miliyan uku daga cikinsu basu da matsuguni.

Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce ta na fuskantar manyan cikas wajen kai tallafin abinci musamman ga yankunan dake karkashin kawanyar soji.

An katse kai abinci da magunguna da wutar lantarki har tsawon kwanaki fiye da dari biyar zuwa ga bangaren dake karkashin ikon 'yan tawaye na birnin Homs.

Karin bayani