An kubutar da 'yan mata 16 masu ciki a Imo

Image caption Sifeto Janar na 'yan sandan Nigeria, Muhammed Abubakar

'Yan sanda a Nigeria sun kai samame inda suka kubutar wasu 'yan mata 16 masu juna biyu, wanda ake shirin sayar da jariransu idan sun haihu.

Jami'an tsaron sun kai samamenne a wani gida dake Owerri babban birnin jihar Imo, bayan samun wasu bayannan sirri sannan suka kubutar da 'yan matan 16.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo, Joy Elomoko ya bayyana cewar shekarun 'yan matan basu wuce 14 zuwa 19 ba.

Elomoko ta kara da cewar 'yan matan sun ce ana basu naira 100,000 idan suka haifi yaran.

Wani mutumi wanda ke da gidan da ake ajiye matan, an tsare shi ana masa tambayoyi.

Jami'an tsaro a cikin 'yan watannin nan sun gano ire-iren wadannan gidaje a kudancin Nigeria inda ake tara 'yan mata masu ciki daga bisani a sayar da jariransu.

Karin bayani