Nakasassu sun yi zanga-zanga a Kano

Image caption Wasu daga cikin nakasassu a Kano

Daruruwan nakasassu ne suka gudanar da wata zanga zangar lumana a majalisar dokokin jihar Kano dan nuna damuwa da amincewa da kudurin dokar hana bara a jihar.

A makon da gabata ne dai majalisar ta amince da kudurin dokar wanda ake saran gwamnan jihar ta Kano zai sa mata hannu nan bada jimawa ba.

Su dai nakasassun na cewa gwamnatin jihar bata maida su mutane ba, domin kuwa babu wani tanadi na koyar da sana'o'i da aka yi musu idan an hana barar, wanda suka ce ta nan kawai suke samun abinci.

Nakasassun sun hada da makafi da kutare da guragu da kuma kurame maza da mata, kuma sun yi zanga zangar ce karkashin jagorancin Aminu Amhad Tudun Wada, mataimakin shugaban kungiyar nakasassu ta kasa.

Karin bayani