An kashe kwamandan Hezbollah

Hassan al-Lakkis
Image caption Isra'ela ta ce ba ta da hannu ko alama a kisan shi

Kungiyar Hezbollah ta ce an kashe daya daga cikin kwamandojinta , a kofar gidansa da ke wajen birnin Beirut na Lebanon.

A Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Isra'ela ce ta kashe Hassan al-Lakkis a lokacin da ya ke dawo wa gida daga aiki da kusan karfe goma sha biyun daren Talata.

Kungiyar ta ce daman a lokuta da dama Isra'ela ta yi kokarin hallaka shi, zargin da Isra'elan ta musanta gaba daya.

Shi dai Hassan al-Lakkis an ce yana daga cikin na hannun daman shugaban kungiyar ta Hezbollah Hassan Nasrallah.