An kashe babban kwamandan Hezbollah

Hassan al-Lakkis
Image caption Isra'ila ta ce ko alama ba ta da hannu a kisan Hassan al-Lakkis

Kungiyar gwagwarmaya a Lebanon - Hezbollah ta ce an kashe mata wani babban kwamandanta a kusa da gidansa da ke wajen birnin Beirut.

Sanarwar da ta fitar ta ce, Isra'ila ce ta kashe Hassan al-Lakkis a lokacin da ya ke koma wa gida daga aiki a cikin dare.

A cewar kungiyar Isra'ila ta dade tanason ta kashe shi.

An bayyana Hassan al-Lakkis a matsayin daya daga cikin na hannun damar shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila, Yigal Palmor ya musanta zargin.

'Zargi kan Saudiyya'

Shugaban kungiyar, Hassan Nasrallah ya zargi kasar Saudi Arabia da kai harin kunar bakin wake a ofishin jakadancin Iran da ke babban birnin kasar Beruit.

Wata kungiya da ke da alaka da al-Qaeda dai ta dauki nauyin kai harin da ya hallaka mutane 23.

Sheik Nasrallah ya shaida wa kafar yada labaran Lebanon ta OTV cewa, ya yi amanna harin da aka kai na da alaka da hukumar leken asarin Saudiyya.

Hezbollah da Iran dai na goyon bayan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, yayin da Saudi Arabiaa ke marawa mayaka 'yan tawaye baya da suke son hanbarar da gwamnatinsa.

Karin bayani