An gano tarin gawarwaki a Mali

Sojojin Mali
Image caption Har yanzu Mali na fama da rikicin 'yan tawaye

A kasar Mali an gano wani makeken kabari da aka binne gawarwaki 20, yayin neman wasu tarin sojoji da suka bata bat tun shekarar da ta wuce.

Masu bincike ne suka gano kabarin a aikin da suke na neman sojojin da suka bata bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar da ta wuce a kasar.

Babban mai gabatar da kara ya sheda wa BBC cewa an gano kabarin ne a garin Diago, da ke da nisan kilomita biyar daga sansanin jagoran juyin mulkin kasar a Bamako.

Akalla sojoji 23 ne da ke biyayya ga shugaban kasar da aka hambarar Amadou Toumani Toure suka bace jim kadan bayan juyin mulkin.

Lokacin da sabon shugaban jagoransu Amadou Sanogo ya zargi sojojin da ke biyayya da laifin yunkurin yin wani juyin mulkin.

An kama Janar Sanago a cikin makon da ya wuce.