Gwamnati ta karawa ASUU wa'adin kwanaki 5

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Gwamnatin Nigeria ta kara wa'adin kwanakin da ta baiwa malam jami'o'in kasar na su koma bakin aikinsu ko kuma a sallame su daga bakin aiki daga ranar laraba 4 ga watan Disamba zuwa ranar Litini 9 ga wannan watan.

Sakataren Hukumar Kula da Jami'oin kasar Julius Okojie shi ya bayyana karin wa'adin ya yin wani taron manema labarai a Abuja.

Gwamnatin ta ce ta karawa malaman saboda baiwa kungiyar ASUU damar jana'izar tsohon shugabanta Farfesa Festus Iyayi wanda ya rasu a hadarin mota.

Tun da farko dai shugaban kungiyar malaman jami'o'in-ASUU Dr Nasir Fagge, ya ce kungiyarsu ba ta damu da wa'adin da gwamnati ta basu ba kuma suna nan kan bakansu na ci gaba da yajin aiki.

Karin bayani