Syria ta ba da damar kai Agaji

Image caption Kayan agaji a Syria za su isa ga wadanda rikici ya rutsa da su

Babbar jami'ar hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valarie Amos ta shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar cewa an sami cigaba wajen kai kayayyakin agaji ga fararen hula 'yan Syria da rikicin kasar ya rutsa da su.

Amos ta ce ta samu damar bawa kwamitin Majalisar Dinkin Duniya shawarar cewa an ga dan ci gaba akan yadda ake gudanar da harkokin mulki a Syria.

Gwamnatin Syriar ta amince da kara ba da takardar izinin shiga kasar wato visa ga ma'aikatan Majalisar hamsin.

Haka kuma ta amince da karin bude sansanonin ba da agaji guda uku a cikin kasar, sai dai kamar yadda Amos ta bayyana ba a basu damar bude sansani a Daara ba inda mutane suka fi bukatar agajin.

Karin bayani