An sake bude filin jirgin sama na Abuja

Image caption Fasinjoji sun yi jugum a filin jirgin sama na Abuja

An mai do da zirgar-zirgar jiragen sama a filin Jirgin saman Abuja bayan katsewa ta kimanin sa'oi ashirin sakamakon lalacewar wani katafare jirgin dakon kaya na kasar Saudiyya kan titin tashi da saukar jiragen na filin jirgin.

An dai kwashe tsawon yinin ranar Alhamis ana kokarin janyen jirgin da ya lalace.

Dubban fasinjoji ne dai sukai cirko cirko a filin jirgin saboda rashin tashi da saukar jirage a lokacin da hukumomi suka bada sanarwar rufe filin jirgin.