Takunkumin Iran na nan daram - Kerry

John Kerry da Benjamin Netanyahu
Image caption Tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinu ta gagara karewa shekara da shekaru

Sakataren harkokin wajen Amurka ya bai wa Fraiministan Isra'ila tabbacin cewa ba za a cire wa Iran manyan takunkumin da aka sa mata ba.

John Kerry ya tabbatar wa Benjamin Netanyahu duk da yarjejeniyar da aka kulla da Iran din ta wucin-gadi akan shrinta na nukiliya muhimman takunkumin na nan.

Bayan wata tattaunawa da Netanyahu a birnin Kudus, Mr Kerry ya ce tsaron Isra'ila shi ne babban abin da Amurka ta sa a gaba a yankin.

Mr Kerry ya je Kudus ne domin wanzar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.