Nelson Mandela ya rasu

Image caption Mandela ya mutu

Tsohon shugaban kasar Afrika a kudu Nelson Mndela ya rasu a daren Alhamis a gidansa dake Johannesburg.

Kwanaki biyu ke nan da iyalansa suka taru a gidan nasa, sannan kuma an ga motocin gwamnati da dama a kofar gidang.

Tsohon shugaban mai shekaru 95 ya shafe kusan watanni uku a gadon asibiti bayan da aka kwantar da shi a watan Yuni saboda ciwon huhu mai tafiya ya dawo.

Nelson Mandela dai shine Shugaban kasar Afrika ta kudu bakar fata na farko wanda mutane da dama suke kallonsa a matsayin uban kasa.

Karin bayani