Mandela: 'Yan Afrika ta Kudu suna jimami

Image caption Dandazon jama'a a harabar gidan Mandela dake Johannesburg

Dandazon al'ummar Afrika ta Kudu sun taru a wajen gidan Nelson Mandela da ke Johannesburg dan girmamawa a gare shi.

Wakilin BBC da ke wajen ya ce mutanen na rera wakokin da aka yi a lokacin gwagwarmaya kan wariyar launin fata.

Wasu daga cikinsu sun zo da kananan yaransu wurin.

Wakilin BBC ya ce bakake da fararen fatan Afrika ta Kudu sun bayyana masa bakin cikin da suke ciki kan mutuwar mutumin da ya cece su.

Ya ce wata mata cikin zubar da hawaye ta shaida masa cewa Mr Mandela ya koya mata darasi kan yafiya.

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ne ya sanar da rasuwar Nelson Mandela din.