An fara cece-kuce kan karawa Jonathan wa'adi

Image caption Ana cece-kuce kan karawa Jonathan wa'adi

A Najeriya, wata sabuwar takaddama ta fara kaurewa a kasar bayan wani furuci da mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya yi.

Sanata Ekweremadu ya ce tsarin wa'adin mulki guda ne zai magance matsalolin da suke dabaibaye harkar mulki a kasar, don haka zai fi dacewa idan aka kara wa shugaban kasa da gwamnoni shekara biyu kafin a gudanar da babban zabe .

Wannan ya haifar da zargin cewa ana kokarin shigo da bukatar Shugaba Jonathan ya sake zarcewa ne kan karagar mulki.

Sai dai wasu 'yan jam'iyyar adawa a Najeriyar na ganin hakan ba za ta sabu ba.

A baya dai an zargi wasu shugabannin a Najeriya da kokarin karawa kansu wa'adi; wanda bai sami nasara ba.

Karin bayani