An kashe mutane 29 a Yemen

yemen attack
Image caption Jami'ai sun ce an shawo kan lamarin bayan wani dan lokaci

A Yemen an kashe mutane 29 tare da jikkata sama da 70 a wani harin kunar bakin wake na bam a mota da aka kai ma'aikatar tsaro a babban birnin kasar Sanaa.

Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun ce bayan harin wasu 'yan bindiga sanye da kayan soji sun bude wuta a kofar ma'aikatar.

Wasu rahotanni sun ce harin ya yi kama da wadanda kungiyar al-Qaeda ke kaiwa.

Amma kuma wani wakilin BBC a birnin ya ce wani minstan gwmnati ya dora alhakinsa a kan mutanen da ke da alaka da tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh.

Wadanda suka mutu sun hada da maharan da wasu ma'aikatan lafiya na wani asbiti da ke cikin ma'aikatar tsaron.

Karin bayani