Dakarun Faransa a Bangui sun fafata kusa da filin jirgi

Image caption Mutane fiye da 100 ne suka mutu a ranar Alhamis

A jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, dakarun Faransa a Bangui sun fafata a kusa sa filin jirgin sama yayinda suke jiran isowar karin sojoji.

Wani mai magana da yawun sojin Faransa ya ce an lalata wata babbar motar soji bayan data bude wuta akan dakaru da kuma fararen hula wadanda suke neman mafaka tare da sojojin Faransa.

Wasu jiragen helicoptan Faransa na kan hanyar zuwa Bangui bayan da majalisar dinkin duniya a ranar Alhamis suka bada umarnin cewa sojoji su kare fararen hula.

Mutane fiye da 100 ne suka mutu a ranar Alhamis a fada tsakanin tsoffin 'yan tawaye da kuma magoya bayan hanbararren Shugaba Francois Bozize

Karin bayani