Rikicin jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Rikicin janhuriyar Tsakiyar Afrika
Image caption Rikicin janhuriyar Tsakiyar Afrika

Sojojin Faransa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun isa garin Bossangoa dake arewacin kasar.

Wuri ne da dubban mutane suka nemi mafaka bayan tsere ma fadan da ake gwabzawa tsakanin kungiyoyin Musulmi da Kirista masu gaba da juna.

A Bangui babban birnin kasar an kashe daruruwan mutane a fadan na addini da ake gwabzawa tun ranar alhamis.

Shugaban kungiyar agaji ta Save the Children Justin Forsyth ya shaidawa BBC cewa a yankunan karkara lamarin yana da matukar munI.

Gwamnatin Faransa za ta girke sojoji dubu daya da dari shidda a kasar , daga dari shiddan da ake da su har zuwa ranar Alhamis.