Mandela ya yi abokai a zaman kurkuku

Image caption Ahmed Kathrada ya nuna jajircewar Mandela a kurkuku

Akasarin rayuwar Marigayi tsohon shugaban Afrika ta Kudu Mr Nelson Mandela ya yi ta ne a gidan yari inda ya shafe kimanin shekaru 27.

A lokacin kuma ya samu abokai da dama cikinsu har da Ahmed Kathrada, wani jagora kuma mai fafitikar yaki da nuna wariyar launin fata wanda ya shafe kimanin shekaru 18 a gidan yari dake Robben Island tare da Mr Mandela da Walter Sisulu.

A shekara ta 2004 ne Mr Kathrada wanda ya fara haduwa da Mr Mandela a shekara ta 1940 lokacin yana dalibi mai koyon aikin lauya, ya rubuta tarihin rayuwarsa da kansa.

Bayan fitowar littafin ne wakilin BBC a birnin Cape Town Mohammed Allie ya tattauna da shi inda ya ce Mr Mandela ya taba fada masa cewa yana ganin wata rana zai zama shugaban kasa.

Karin bayani