Ana ci gaba da alhinin mutuwar Mandela

Image caption Ana ta alhinin mutuwar gwarzo Mandela

Kwana guda da sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela, amma Har yanzu dandazon al'umar kasar na kai kawo a tituna dan nuna alhinin mutuwar sa.

A wajen gidan sa da Soweto mutane sun shafe tsahon daren jiya su na gudanar da addu'o'i tare da ajiye furanni, ya yin da wasu ke rera wakoki da taka rawa don tunawa da rayuwarsa.

A birnin Cape town ma mutane sun taru a inda Mr Mandela ya yi jawabi na farko bayan fitowarsa daga gidan yari,inda ya shafe shekaru 27.

Za a ci gaba da nuna alhinin mutuwar tasa saboda irin rawar da ya taka kan ceto al-umma.

Karin bayani