Faransa za ta horas da sojojin Afrika

Dakarun Sojin Afurka
Image caption Dakarun Sojin Afurka

An kammala taron koli kan tsaro a birnin Paris, inda shugaban kasar ya bukaci a kafa wata rundunar mayar da martani cikin gaggawa a Afrika, cikin watanni masu zuwa.

Francois Hollande ya shaidawa shugabannin Afrika cewa a shirye Faransar take ta horas da sojojin Afrika dubu ashirin a shekara, har tsawon shekaru biyar, masu zuwa, sannan su samar ,masu da makamai da kuma kayan aiki.

Ya kuma bukaci sauran kasashen Turai da su bada tasu gudunmawar yana cewa ta'addanci bai san kan iyakar wata kasa ba.