Philiphines ta soma farfodawa

Tacloban Philiphines
Image caption Tacloban Philiphines

Wata daya bayan mahaukaciyar guguwar nan da ta yi kaca-kaca da tsakiyar kasar Phillipines akwai alamun dake nuna cewar sannu a hankali kasar na farfadowa.

Fiye da mutane dubu biyar da dari biyar ne suka hallaka a lokacin a yayinda wasu miliyoyi suka rasa gidajensu da hanyoyin neman abincinsu.

A birnin Tacloban daya daga cikin wuraren da mahaukaciyar guguwar ta fi yin barna, gwamnati da hukumomin ba da agaji suna biyan mutanen yankin kudade a ayyukan gyara muhallin.

Sai dai sun ce sake gina wuraren zai dauki a kalla shekaru ukku.

Guguwar ta Haiyan ta kuma yi barna a wasu sassa na kasar da kasashe makwabta.