Kungiyoyin agaji sun biya Al shabab kudi

Somalia
Image caption Mayakan kungiyar Al shabab

Wani sabon rahoto ya ce kungiyoyin agaji sun biya kungiyar Al Shabab kudi don bayar da agaji ga 'yan kasar Somalia masu fama da yunwa a shekarar 2011.

Rahoton wanda wata cibiyar nazarin ci gaban kasashen waje ta bayar ya gano cewar kungiyar ta Al shabab ta nemi kungiyoyin ba da agajin su biya ta kudade kafin su shiga yankunan dake karkashin ikonta.

Mutane fiye da dubu 300 ne suka mutu lokacin da kasar ta yi fama da matsananciyar yunwar.

Rahoton ya ce kungiyar Al shabab ta nemi kungiyoyin agaji su bayarda abin da ta kira kudin rajista da ya kai dala dubu 10.

Haka kuma an samu batutuwa da dama inda kungiyar ta Al shabab ta ce ita ce za ta raba kayayakin agajin da kanta, alhali kuwa ta kan bar ma kanta da dama daga cikin kayayakin domin biyan bukatunta.