Thailand za ta rusa Majalisar Dokoki

Thailand
Image caption Masu zanga-zanga a kasar Thailand

Pirai Ministan Thailand Yingluck Shinawatra ta sanar da cewa za ta rusa Majalisar Dokokin kasar bayan jerin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin da aka yi a birnin Bangkok.

A jawabin da ta yi ta talbijin, Ms Yingluck ta ce za ta gudanar da sababbin zabuka nan ba da jimawa ba.

Ta kuma ce akwai gungun mutane da ke adawa da gwamnatinta kuma ba ta son a sake samun asarar rayuka.

Kakarshin ka'idojin zabe na kasar Thailand, ya kamata a gudanar da zaben Majalisar Dokoki bayan watanni biyu da rusa Majalisar.

Sai dai babu tabbas a kan ko masu zanga- zangar zasu amince da wanan mataki, saboda abin da suke so shi ne a sauya tsarin mulkin demokradiyar kasar baki daya.