Zanga-zanga a kasar Ukraine

Masu zanga-zanga a kasar Ukraine
Image caption Masu zanga-zanga a kasar Ukraine

Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a Ukraine sun tumbuke mutum mutumin jagoran juyin juyahalin kasar Rasha, wato Lenin, a lokacin zanga zanga mafi girma a birnin Kib cikin shekaru tara.

Dandalin Indipenda yayi cikar-kwari da dubban daruruwan jama'a dake nuna takaicinsu kan matakin da shugaba Viktor Yanukovych ya dauka na kin rattaba hannu kan wata yarjejeniyar cinikayya da tarayyar Turai, maimakon haka ya zabi karfafa dangantaka da Rasha.

An tsaurara matakan tsaro a kewayen gine gine gwamnati dake kusa da dandalin.

Wani wakilin BBC ya ce ana zanga-zangar ne cikin lumana, amma kuma da nuna jajircewa.