Yajin aikin ASUU na ci gaba da tasiri

Image caption Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan

Duk da cikar wa'adin da gwamnatin Nigeria ta baiwa kungiyar malaman jami'o'in kasar- ASUU don ta koma bakin aiki, rahotanni sun nuna cewar kawo yanzu galibin jami'o'in kasar na ci gaba da kasancewa a rufe.

Gwamnatin Najeriyar dai ta baiwa malaman jami'o'in kasar wa'adin ko su koma aiki ranar Litinin ko kuma su dauki kan su a matsayin korarru.

Wakilin BBC ya ziyarci jami'ar Bayero dake Kano inda ya ga galibin ajujuwa a rufe kuma babu dalibai a cikin makarantar.

Wani malami a jami'ar ya ce ba za su koma aiki ba har sai kungiyar ASUU ta basu umurnin yin hakan.

Malaman jami'in dai sun shafe watanni shida suna yajin aiki, da nufin matsawa gwamnati lamba ta cika wasu alkawura da bangarorin biyu suka yi shekaru hudu da suka gabata.

Karin bayani