Obama ya bukaci zaman lafiya a Afrika ta tsakiya

Central African Republic
Image caption Yan gudun hijira a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Shugaba Obama ya yi kiran da a farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin wucin gadi ta kasar ta kame dukkan mutanen dake aikata miyagun laifukka.

Kiran ya zo ne bayan Sakataren tsaron Amurkar Chuck Hagel ya amince da bukatar da Faransa ta gabatar ta yin amfani da jiragen jigila 2 na Amurka.

Za a yi amfani da jiragen ne wajen kwasar sojoji dari 850 na Burundi daga Burundin zuwa Jamhuriyar Afrikar ta Tsakiya.

Sojojin za su yi aiki ne kafada-da-kafada da dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afrika wajen dakatar da fadan na addini.